News
Firayim Ministan Albaniya Ya Ce Ministar Kirkirarriyar Basirar Al Ta Samu ‘Juna Biyu’ Da Jariran Dijital 83
Firayim Ministan Albaniya, Edi Rama, ya bayyana cewa Diella — ministar kirkirarriyar basira (AI) ta farko a duniya — tana da juna biyu da jariran dijital guda 83.
Wannan mataki zai bai wa kowanne ɗan majalisar jam’iyyar Socialist mataimakin AI domin bibiyar zaman majalisa, tattara bayanai, da bayar da shawarwari ga ƴan majalisa.
Firayim Ministan ya bayyana hakan ne yayin taron Global Dialogue (BGD) da aka gudanar a birnin Berlin ranar Lahadi.
>“Mun ɗauki babban haɗari da Diella, amma abin ya tafi daidai. Don haka, karo na farko Diella tana da juna biyu, kuma tana ɗauke da jariran dijital 83,” in ji Rama.
Ya ƙara da cewa kowanne daga cikin waɗannan jariran AI zai kasance mataimaki ne da zai halarci zaman majalisa, ya ɗauki bayanan da suka gudana, sannan ya sanar da ƴan majalisa duk wani abu da suka rasa.
“Waɗannan jariran za su mallaki ilimin mahaifiyarsu, Diella, kuma za su taimaka wajen tabbatar da nagartaccen gudanar da ayyuka a majalisa,” in ji shi
A tarihin duniya, Diella ce ministar kirkirarriyar basira ta farko da aka ƙirƙira gaba ɗaya daga lambar kwamfuta da hoton dijital, wadda ke bayyana a matsayin mace a cikin rigar gargajiya ta Albaniya.
