Connect with us

News

Kungiyar “One Kano Agenda” Ta Yi Allah-wadai Da Ƙoƙarin NUPENG Da PENGASSAN Na Durkusar Da Matatar Man Dangote

Published

on

IMG 20251027 WA0008

‎Kungiyar One Kano Agenda ta bayyana rashin jin daɗinta kan barazanar da ƙungiyoyin ma’aikata na NUPENG da PENGASSAN suka yi wa Matatar Man Dangote, tana mai cewa hakan na iya zama barazana ga tattalin arzikin ƙasa da kwarin gwiwar masu zuba jari.

‎A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce tana gozon baya da cikakken goyon baya ga Matatar Dangote, wacce ta bayyana a matsayin ginshiƙin ‘yancin tattalin arziki da ci gaban masana’antu a Najeriya.

Advertisement

‎Yadda Sanata Barau Jibrin Ke Ƙarfafa Tsaron Ƙasa Ta Hanyar Tallafa Wa Matasa A Mazabarsa

‎Kungiyar ta ce, “Matatar Dangote ba kawai kamfani na mutum ɗaya ba ne, amma alama ce ta jajircewar Najeriya wajen rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje, da farfaɗo da masana’antu, da ƙarfafa tattalin arziki.”

‎Ta ƙara da cewa, “Matatar man Dangote na nuna yadda jarumtaka da hangen nesa da kishin ƙasa za su iya sauya yanayin tattalin arzikin ƙasa da rayuwar al’umma.”

Advertisement

‎Kungiyar ta yaba da irin rawar da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da wasu manyan ‘yan majalisar tarayya suka taka wajen kare martabar wannan babbar masana’anta.

‎Ta ce, “Idan gwamnati na magana kan masana’antu, Dangote yana gina su. Idan ana magana kan noma, shi yana samar da takin zamani. Yayin da wasu ke tattaunawa, shi yana aiki.”

Advertisement

‎Kungiyar ta bayyana maganganun ƙungiyoyin NUPENG da PENGASSAN kan Matatar Dangote a matsayin “abin takaici,” tana mai cewa irin wannan barazana na iya jefa dubban ma’aikata cikin rudani da hana sabbin zuba jari a ƙasar.

‎“Wadannan ƙungiyoyi da ya kamata su kare ma’aikata, suna kusan zama barazana ga rayuwar ma’aikatan da suke cewa suna karewa,” in ji ƙungiyar.

Advertisement

‎Kungiyar ta jaddada cewa ya kamata ƙungiyoyin ƙwadago su zama abokan haɗin gwiwa wajen haɓaka masana’antu, ba masu tayar da tarzoma ba.

‎“Duk wanda ya kai hari ga Matatar Dangote, to ya kai hari ga ma’aikata da tattalin arzikin ƙasa gaba ɗaya,” in ji sanarwar.

Advertisement

‎Kungiyar ta kuma yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya bai wa Kamfanin Man Dangote cikakken kariya, tana mai cewa hakan zai nuna yadda gwamnati ke daraja jarin cikin gida da ƙoƙarin samar da cikakken ‘yancin tattalin arziki.

‎Ta ce, “Alhaji Aliko Dangote ba kawai ɗan kasuwa ba ne — ginshiƙi ne na ƙasa wanda ya zuba jari inda wasu suka kasa, ya gina masana’antu inda ake dogaro da ƙasashen waje.”

Advertisement

‎A ƙarshe, ƙungiyar ta ce tana tsaye cikakke tare da Alhaji Aliko Dangote da Kamfanin Man Dangote, tana kira ga ‘yan Najeriya da su kare kamfanin a matsayin alamar kishin ƙasa da haɗin kai.

‎“Wanda ya raunana Kamfanin Man Dangote, ya raunana Najeriya,” in ji ƙungiyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending