News
Yadda Sanata Barau Jibrin Ke Ƙarfafa Tsaron Ƙasa Ta Hanyar Tallafa Wa Matasa A Mazabarsa
DAGA ABBA ANWAR, KANO
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin (CFR), ya sake tabbatar da jajircewarsa wajen inganta tsaron ƙasa ta hanyar ƙarfafa matasa da kuma haɓaka haɗin kai tsakaninsu da hukumomin tsaro a yankinsa na Kano ta Arewa da ma ƙasar baki ɗaya.
A wani sabon mataki da ya ɗauka domin ƙarfafa hukumomin tsaro, Sanata Barau ya taimaka wajen samar da guraben aikin gwamnati ga matasa 120 daga mazabarsa — a matsayin jami’an ‘yan sanda, jami’an Hukumar EFCC da kuma jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service).
Domin taya sabbin jami’an murnar wannan nasara, Sanatan ya shirya musu taron liyafa a Otal ɗin Bristol Palace da ke Kano a ranar Lahadi.
“Na halarci liyafar domin taya sabbin jami’an ‘yan sanda, EFCC da hukumar kashe gobara murna. Na tunatar da su cewa wannan aiki kira ne zuwa hidima ga ƙasa – domin kare rayuka, dukiya da tabbatar da adalci,” in ji Sanata Barau.
Ya ƙara da cewa wannan nasarar ta nuna yadda gwamnati ke ƙoƙarin samar da tsaro mai ɗorewa ta hanyar haɓaka ƙwararrun matasa daga sassa daban-daban na ƙasa.
Sanatan ya kuma jaddada muhimmancin ilimi ga waɗannan sabbin jami’ai, inda ya ƙarfafa su da su ci gaba da karatu nan gaba.
“Na shawarce su da su ci gaba da karatunsu. Na kuma tabbatar musu cewa asusun tallafina (foundation) zai ɗauki nauyin biyan kuɗin rajistarsu a Jami’ar NOUN da sauran makarantu masu inganci,” in ji shi.
A baya, Sanata Barau ya bayar da babura 1,000 ga rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano domin taimaka musu wajen gudanar da ayyuka a yankuna daban-daban na jihar — inda 700 aka bai wa Kano ta Arewa, yayin da sauran 300 suka tafi Kano ta Tsakiya da ta Kudu.
Haka kuma, ya ba da motoci 22 na aiki ga rundunar ‘yan sanda, tare da ɗaukar nauyin gyaran hedikwatar ‘yan sanda ta Bompai, aikin da ya kai sama da Naira Biliyan Daya (₦1bn).
A cewar Barau, duk waɗannan ayyuka suna nuna cewa ya ɗauki tsaro a matsayin ginshiƙin ci gaban ƙasa.
“Na gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewarsa wajen ƙarfafa tsarin tsaro a ƙasar nan,” in ji shi.
Sanata Barau ya kuma yaba wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) bisa gaggawar da ya nuna wajen tura ƙarin jami’ai zuwa wasu yankunan Kano ta Arewa da ke fuskantar matsalolin tsaro.
Wani babban abin lura kuma shine, wato shi Sanata Barau mutum ne da ya kara samun karfi da gogewa da tsayuwar daka. Kamar dai yadda tarihin kasashe ya nuna cewar, kasashen da su ka sha gwagwarmaya da fadi-tashi sun fi zama dakakku kuma jajirtattu a harkar su ta rayuwa, ta yau da kullum.
Misalin irin wadannan kasashe sune Kasar Jamus da Japan bayan yakin duniya na biyu. Da kuma kasar Rwanda bayan kare yakin kisan kiyashi da a ka dade a na yi a kasar. Da kuma Korea ta Kudu, bayan yakin Korea.
A takaicen takaicewa dai Sanata Barau shine Jamus din da Japan din da Rwanda din da kuma Korea ta Kudun.
Masu lura da al’amura sun bayyana cewa Sanata Barau — wanda ake kira Maliya — na daga cikin fitattun ‘yan siyasa masu kishin ƙasa da hangen nesa, waɗanda ke ɗaukar tsaro da ci gaban matasa a matsayin manyan ginshiƙai na cigaban ƙasa.
Tsarin siyasar sa ya yi daidai da manufar “Renewed Hope Agenda” ta Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda ke mayar da hankali kan tsaro, ci gaban al’umma da taimakon matasa.
A cewar wasu masu sharhi, irin wannan jajircewar Sanata Barau ta tabbatar da matsayin sa a matsayin ɗaya daga cikin manyan shugabanni masu kishin ƙasa da nagartar shugabanci a Najeriya.
Abba Anwar ya rubuto daga Kano
Litinin, 27 ga Oktoba, 2025
