Connect with us

News

Yaƙin Yemen: Iran da Saudiyya sun yi na’am da tsagaita wuta

Published

on

Saudiyya da Iran sun yi na’am da tsagaita buɗa wuta a Yemen da ta soma aiki a yau kuma ake fatan ta ci gaba tsawon wata biyu wacce majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta.

Advertisements
Advertisements

Yarjejeniyar ta soma aiki daga ranar Asabar, yarjejeniyar tsagaita wuta ta ƙasa baki ɗaya ta farko a yaƙin Yemen na shekara bakwai tun 2016

Advertisements

Ministan harakokin wajen Saudiyya wacce ke goyon bayan gwamnatin Yemen, ya jaddada cewa yarjejeniyar na daga cikin manufar tabbatar da zaman lafiya da Saudiyya ta gabatar a bara.

Iran wacce ke goyon bayan mayaƙan Houthi, ta bayyana fatan cewa wannan zai kai ga haifar da tsagaita wuta ta dindin domin samar da mafitar siyasa a rikicin Yemen.

Advertisements
Advertisements
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending