News
Yadda Rashin Wutar Lantarki Ke Ruguza Kasuwanci A Najeriya.
A cikin ’yan watannin nan ana fama da matsalar rashin man fetur da gas, matsalar ta yi naso a kan rashin wutar lantarki, inda a jihohi da dama ke fama da rashin wutar lantarki.
Jaridar Aminiya ta tuntubi bangarorin ’yan kasuwa da masana kan yadda rashin wutar lantarkin yake ruguza al’amuran kasuwanci da na yau da kullum.
Harkokin kasuwanci a Jihar Kano suna ci gaba da samun koma-baya saboda rashin isasshiyar wutar lantarki da hakan ya janyo karin tsadar kayayyaki, a gefe guda kuma ya haifar da karancin riba.
Hakan ya janyo mafi yawan ’yan kasuwa da kamfanoni suka dan yi gyaregyare wajen gudanar da ayyukansu domin neman mafita game da halin da ake ciki.
Wani tela da Aminiya ta zanta da shi ya ce rashin wutar lantarki ya janyo masa koma baya a ayyukansa domin akwai kekunansa da sai da wutar lantarki suke aiki wanda kuma “A yau ga shi man fetur ba ya samuwa ballantana mu yi amfani da shi.
“Hakan ya tilasta na ajiye aikin gaba daya saboda idan na sayi man fetur na yi aiki da shi ba zan fita daga kudin aikin da za a biya ni ba.
Idan kuma na kara kudi a kan kudin dinkin da aka saba biya na tabbas ba za mu daidaita da abokan huldana ba,” inji shi.
Ya ce a yanzu haka lamarin ya janyo cushewar aiki a wurinsa inda yake hangen lamarin zai shafi aikinsa na Sallah.
Ya ce “Abin da yake damuna shi ne aiki zai cunkushe min saboda baya ga dinkunan da ke gabana a yanzu kuma mutane har sun fara kawo dinkunan Sallah.
Idan ba Allah ne Ya sa aka samu wutar lantarkin nan ta daidaita ba, to babu shakka akwai matsala.”
Shi ma wani kamfanin ruwan leda ya ce rashin wutar lantarki ya janyo ya dakatar da ayyukansa na wani lokaci.
Wata majiya da ta nemi a boye sunanta a kamfanin ruwan tace shugaban kamfanin ya shaida wa ma’ikatansa cewa ba za iya ci gaba da yin aiki ba saboda ba ya samun riba a kan abin da yake yi a kullum.
Shugaban ya shaida mana cewa saboda dizal ya yi tsada idan har suka yi aiki da shi ba su kirga riba sai faduwa. Kin san kuma kasuwanci don riba ake yi,”inji shi.
Ya ce a yanzu haka saboda tsayawar kamfanin ya janyo ma’aikatan kamfanin sun zama masu zaman kashe wando.
Majiyarmu ta kara da cewa ko da a ce kamfanin zai dawo da aikinsa to dole sai idan an samu gyaruwar wutar lantarki. Wata da ke gudanar da sana’ar gyaran gashi Hajiya Habiba Balogun ta bayyana cewa rashin wutar lantarki ya janyo kasuwancinta ya tsaya cak.
Duba da rashin wutar lanatarki da kuma wuyar man fetur za ki ga aikinmu ba ya tafiya yadda ya kamata. Idan mun samu man fetur mu yi aiki idan ba mu samu ba, sai dai mu zauna mu yi hira a shago,” inji ta.
Ta ce a yanzu sun fi mayar da hankali wajen yin kitso da kunshi saboda halin da suke ciki. “Kin ga a da saboda muna aiki sosai ba mu tsayawa yin kitso ko kunshi saboda daukar lokaci da suke yi.
“Amma yanzu da aikin gyaran gashin ya zama sai a hankali, hakan ya sa muke neman mutanen da za mu yi wa kitso. Kin san kiran abokan hulda nake yi a waya idan suna bukatar kitso ko kunshi su zo a yi musu.
“Hakan yana taimaka mana sosai domin ba mu rasa dan abin da za mu sa a bakin salati har ma mu samu na biyan mota,” inji ta.
