Connect with us

Politics

BAYAN RIKICI: Jam’iyyar Labour Party Ta Komawa Hannun Ƙungiyoyin Ma’aikata A Najeriya 

Published

on

IMG 20260307 WA0083

DAGA KWAMARED ABBAS IBRAHIM

Bayan watanni na rikicin siyasa da shari’a, alamu na nuna cewa Jam’iyyar Labour Party (LP) na komawa karkashin ikon asalin masu kafa ta – wato ƙungiyoyin ma’aikata da kuma magoya bayan talakawa a Najeriya.

Advertisement

‎Tun da farko an kafa jam’iyyar ne da goyon bayan Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da kuma Trade Union Congress (TUC) domin samar wa ma’aikata, ƙwararru da sauran ‘yan ƙasa wata kafa ta siyasa da za ta wakilci muradunsu.

Yadda Tashin Gobarar Kasuwar Singer Ke  Barazana Ga Ci gaban Kasuwannin Wasu A Kano

Advertisement

‎Sai dai a ‘yan shekarun nan karuwar farin jinin jam’iyyar ya jawo hankalin wasu ‘yan siyasa, lamarin da ya haifar da rikice-rikicen cikin gida kan shugabanci a jam’iyyar.

‎Rikicin ya kai har gaban Kotun Ƙoli ta Najeriya, wadda a hukuncin da ta yanke ranar 5 ga Afrilu, 2025, ta jaddada cewa wajibi ne jam’iyyun siyasa su gudanar da harkokinsu bisa kundin tsarin mulkinsu da kuma ka’idojin dimokuraɗiyya na cikin gida.

Advertisement

‎Shugabannin ƙungiyoyin ma’aikata sun ce wannan ci gaba na ba da damar sake gina jam’iyyar bisa akidar ta ta farko wadda ta mayar da hankali kan adalci ga al’umma da shugabanci mai kula da bukatun jama’a.

‎Masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar sun kuma jaddada bukatar ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida, tare da tabbatar da gudanar da zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci domin hana sake samun rikici a nan gaba.

Advertisement

‎Sun kuma ce ya kamata a bai wa ƙungiyoyin ma’aikata muhimmiyar rawa a tsarin yanke shawara, tare da kafa sahihin tsarin tantance mambobi da kuma tsauraran matakan ladabtarwa domin dakile shigar masu anfani da damar siyasa kawai.

‎Baya ga gyaran cikin gida, shugabannin jam’iyyar na ganin babban aikin da ke gabansu shi ne sake farfaɗo da tsarin jam’iyyar a matakin ƙasa, ta hanyar haɗa ƙungiyoyin ƙwadago, matasa, ƙwararru da kuma kungiyoyin al’umma domin gina jam’iyyar a matsayin babbar ƙungiyar siyasar jama’a.

Advertisement

‎Masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce watanni masu zuwa za su nuna ko jam’iyyar za ta iya ƙarfafa tushenta tare da ci gaba da zama wata kafa ta siyasa da ke wakiltar muradun ma’aikata da talakawan Najeriya.

‎Kwamared Abbas Ibrahim, ya ce wannan lokaci wata dama ce ta dawo da manufar da aka kafa jam’iyyar a kanta domin kare muradun ma’aikata da talakawa.

Advertisement

‎Ya ƙara da cewa, dole ne a ci gaba da yin gyare-gyare da kuma ƙarfafa wayar da kai domin kare jam’iyyar daga duk wani yunƙurin kwace ta a nan gaba.

 

Advertisement

Kwamared Abbas Ibrahim Mataimakin sakataren NLC a Jihar Kano, wanda kuma shi ne amintaccen mamba na ƙasa a shiyyar A na Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ),

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending