Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Ƙungiyar Masu Masu Satar Adaidaita Sahu A Kano

Published

on

FB IMG 1759160530529 768x512 (1)

Rundunar Ƴan sanda ta kama mambobin wata ƙungiya ta mutum uku da ke satar adaidaita sahu (keke napep) tare da kwato guda takwas da suka sace a Jihar Kano.

Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar, Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa lamarin ya fara ne a ranar 26 ga Maris, lokacin da jami’an da ke aiki a Sashen ’Yan Sandan Kwakwachi, yayin sintiri a kan titin Airport a Kano, suka tare wani Abubakar Sidi, mazaunin ƙauyen Kunkumi a Jihar Kaduna, yana tuka wata adaidaita sahu mai lamba NSR 85 WD, Karota No. KMC 1084.

Advertisement

Jami’an Tsaro Sun Cafke Sojan Bogi Da Wasu Biyar Kan Rikicin Jos

Kiyawa ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan ya kasa bayar da gamsasshen bayani kan yadda ya samu adaidaita sahun, sannan aka miƙa shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na rundunar bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sanda domin ci gaba da bincike.

Advertisement

Ya ƙara da cewa bincike ya nuna wanda ake zargin ya yaudari mai adaidaita sahu a kan titin Emir Palace a Kano, sannan ya haɗa baki da sauran mambobin ƙungiyarsu wajen ƙwace masa ababen hawansa.

Daga bisani, an kama wasu abokan aikinsa biyu, wato Abba Babura da Babangida Haruna, tare da ƙwato ƙarin adaidaita sahu guda bakwai da suka sayar a garin Babura na Jihar Jigawa.

Advertisement

Rundunar ’yan sanda ta shawarci al’umma, musamman masu tukin adaidaita sahu, da su kasance masu lura da taka-tsantsan yayin hulɗa da fasinjoji.

“Mun shawarci jama’a da kada su karɓi abin sha ko kyauta daga baƙi, sannan muna kira ga duk wanda ke da bayani kan duk wani motsi na zargi da ya kai rahoto ga hukumomi.

Advertisement

“Har ila yau, rundunar na kira ga duk wanda aka sace masa adaidaita sahu ta irin wannan dabara da ya duba hotunan da aka wallafa, sannan ya garzaya ofishin PPRO a shelkwatar ’yan sanda ta Bompai a Kano ko ya tuntubi jami’in bincike (IPO) ta lambar 07010161372,” in ji Kiyawa.

Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da wannan aiki, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin yaƙi da laifuka da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending