Labarai
Jami’an NDLEA Sun Kama Kilo 748 Na Tramadol A Hanyar Benin zuwa Legas

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen Jihar Edo ta sanar a ranar Litinin cewa ta kama magungunan, ciki har da tramadol mai nauyin kilo 748.02, a kan babbar hanyar Benin zuwa Legas.
Kwamandan NDLEA na Jihar Edo, Mitchell Ofoyeju, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa yayin da yake gabatar da nasarar aikin rundunar ga manema labarai a Benin.
Siyasa Ce Ta Fi Dacewa Da Malamai Ba Kamasho Ba —Malam Ibrahim Khalil
Ya ce: “A ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026, ƙoƙarin rundunar na yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ya kai ga kama wata babbar mota kirar Mercedes-Benz mai ɗauke da tambarin Kungiyar ‘Yan Kwadago ta Kasa (NLC) mai lambar NLC 146 FC.
“An gano cewa motar na ɗauke da kwalaye 95 masu ɗauke da kapsul da ƙwayoyi har miliyan 1.196 na magungunan da ake amfani da su ga masu taɓin hankali a Asibitin kula da lafiyar kwakwalwa, waɗanda aka ɗauko su daga Legas zuwa Onitsha a Jihar Anambra.
“An kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi mambobin ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi ne, Osagie Igbinibo mai shekaru 43 da Omijie Malik mai shekaru 44, dangane da wannan kamen.”
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai6 days ago
An Kashe Mutane 418, An Yi Garkuwa Da 227 Cikin Watanni Biyu A Nijeriya — Rundunar Ƴansanda
