Connect with us

News

Shin Da Gaske Gwamnatin Shugaba Tinubu Za Ta Fara Karbar Harajin Siya Da Saka Sola?

Published

on

SOLAR PANEL 1536x1152

Jita-jitar cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin fara karɓar haraji ga masu amfani da na’urorin hasken rana (solar) ta bazu a kafofin sada zumunta, lamarin da ya janyo muhawara a tsakanin jama’a.

Sai dai bayanai daga majiyoyi masu tushe sun nuna cewa, a halin yanzu, babu wata doka a hukumance da ta tilasta wa masu amfani da solar a gidajensu biyan wani haraji na musamman. Haka kuma, ba a bukatar izini daga gwamnati kafin saye ko girka irin waɗannan na’urori domin amfanin gida.

Advertisement

Shin Da Gaske Gwamnatin Shugaba Tinubu Za Ta Fara Karbar Harajin Siya Da Saka Sola?

Rahotanni sun ce asalin wannan jita-jita na da alaƙa da wasu ƙa’idoji da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta tsara, waɗanda suka fi shafar manyan kamfanoni da masana’antu masu amfani da manyan tsarin solar masu ƙarfin gaske, musamman waɗanda suka haura megawatt 1.

Advertisement

A irin waɗannan lokuta, ana buƙatar kamfanonin su yi rajista tare da bin ƙa’idoji kafin fara samar da wutar lantarki. Haka kuma, akwai tsarin haɗa solar da wutar lantarkin gwamnati, wanda ke bai wa masu amfani damar sayar da ragowar wuta, amma wannan ma na buƙatar shigar da mita da bin wasu dokoki na musamman.

Bugu da ƙari, an samu ƙorafe-ƙorafe kan karin harajin shigo da kayayyakin solar daga ƙasashen waje, ciki har da batir da fanel, wanda ake dangantawa da tsarin Import Adjustment Tax. Wannan mataki na iya ƙara farashin kayayyakin a kasuwa, amma ba haraji ba ne kai tsaye kan masu amfani da solar a gidajensu.

Advertisement

Masana sun ce yawancin bayanan da ke yawo sun samo asali ne daga rashin fahimta ko kuma haɗa bayanai da suka shafi manyan kamfanoni da na talakawa.

A ƙarshe, ana shawartar jama’a da su rika tabbatar da sahihancin labarai kafin yaɗa su, musamman a shafukan sada zumunta, domin gujewa yaɗa bayanan da ba su da tushe.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending