Connect with us

News

Kuskuren Harin Dakarun Sojin Sama Ya Sake Hallaka Tarin Fararen Hula A Neja

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Rahotanni daga jihar Neja sun ce wani harin sojin Najeriya ta sama ya kashe fararen hula da dama a matsugunan Guradnayi da ke gab da garin Kasasu a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar da ke tsakiyar ƙasar.

Wannan na matsayin ƙari kan tarin hare-haren da sojin Najeriya ke kaiwa bisa kuskure da ke sabbaba asarar ɗimbin rayukan fararen hular da basu ji ba basu gani ba musamman a jihohin da ke fama da ayyukan ta’addanci.

Advertisement

Jami’an NAPTIP Sun Kama Gidan Marayun Dake Siyar Da Yara Kanana

Majiyoyi sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Lahadi inda bayanai ke cewa wasu iyalan gabaki ɗaya suka rasa rayukansu a wannan hari yayinda kusan dukkanin gidajen da ke Guradnayi suka rasa aƙalla mutum guda zuwa sama daha ahalinsu.

Advertisement

Wani mazaunin Kusasu Auta Awododo ya shaidawa wata jaridar Najeriyar cewa da misalin ƙarfe 5 na asubahi ne aka kai harin na yau yana mai cewa a gidan wani ɗan uwansa kaɗai mutane 12 suka mutu sanadiyyar harin sojojin Najeriyar.

A cewar Mr Awododo galibin waɗanda harin Sojojin ya rutsa da su mutane ne da suka tserewa hare-haren ƴan ta’adda a Kusasu.

Advertisement

Wata majiya ta daban ta ce harin Sojin Najeriyar ya faru ne bayan wuce ayarin ƴan bindiga haye a babura ta cikin ƙauyukan da ke gab da Kusasu waɗanda sojoji ke biye da su.

Majiyar ta ce da farko sojojin sun fara jefa bom guda a kogin Kusasu gabanin sake jefa bom na biyu a Guradnayi wanda shi ne ya yi ɓarnar.

Advertisement

Har kawo yanzu dai rundunar Sojin Najeriya ba ta ce komai game da wannan hari ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da sojoji ke kuskuren hari tare da kashe ɗimbin fararen hula a wannan yanki ba inda a shekarar 2022 wani harin sojin sama ya kashe ƙananan yara 6 a ƙauyen Kurebe yayinda watanni 5 tsakanin wani harin na daban ya sake kashe fararen hula 8 duk dai a ƙauyen.

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending