Connect with us

News

Rikici Ya Kunno Kai A KUST Wudil Yayin Da ASUU Ta Ki Amincewa Da Sabbin Dokoki

Published

on

Aliko Dangote University of Science and Technology ADUSTECH (1)

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano da ke Wudil (KUST Wudil), ta yi watsi da wasu sabbin takardun gudanarwa da mahukuntan jami’ar suka amince da su, tana mai zargin cewa an samar da su ne ba tare da bin ka’idojin doka da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

Matsayar ta fito ne bayan taron majalisar kungiyar da aka gudanar ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, inda ta bayyana damuwa kan abin da ta kira yunkurin kakaba wasu dokoki da za su iya yin illa ga ci gaban jami’ar da kuma walwalar ma’aikata.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Kama Mutane 46 Yan Kasashen Waje Bisa zargin Suna Zaune Tare Da Takardun Izinin Zama Ba

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce duk da kokarin da gwamnatin Jihar Kano ke yi wajen inganta ilimi da walwalar ma’aikatan jami’ar, matakan da mahukuntan KUST suka dauka sun saba wa tanade-tanaden dokar jami’ar.

Advertisement

ASUU ta yi zargin cewa an amince da sabbin takardun ne ba tare da bin Sashe na 21 na Dokar Gyaran KUST ta shekarar 2017 ba, wanda ya tanadi hanyoyin da ya kamata a bi wajen yin gyara ko sauyi a irin wadannan muhimman takardu.

Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa majalisar gudanarwar jami’ar da ta amince da sabbin dokokin ba ta cika sharuddan da doka ta gindaya ba, saboda rashin gudanar da zaman majalisar dattawan jami’a (Senate) domin zaben wakilinta a majalisar gudanarwar.

Advertisement

Haka kuma, ASUU ta zargi mahukuntan jami’ar da kasa fitar da rahoton binciken kudaden jami’ar na sama da shekaru uku, da kuma rashin gudanar da wasu muhimman tarurrukan da doka ta tanada.

Bayan tattaunawa mai zurfi, majalisar kungiyar ta yanke shawarar yin Allah-wadai da sake duba takardun, tare da yin watsi da su gaba daya. Ta kuma umarci mambobinta da kada su amince ko amfani da sabbin takardun har sai an warware takaddamar.

Advertisement

Kazalika, kungiyar ta nemi amincewar Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na ASUU domin fara aiwatar da matakin da ta kira “Active Non-Compliance”, har sai mahukuntan jami’ar sun magance korafe-korafen da ta gabatar.

Sanarwar ta samu sa hannun shugaban reshen kungiyar, Dakta Yusuf Ahmad, da sakataren reshen, Dakta Abubakar Ibrahim Tukur.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending