Connect with us

News

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Shugaban Makaranta A Oyo

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban Makarantar Firamare ta Nomadic da ke Igbojaye, Budo, a ƙaramar hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo, Kolawale Mathew Owoade, mai shekaru 60.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, tsakanin ƙarfe 5:00 zuwa 6:00 na yamma, yayin da shugaban makarantar ke kan hanyarsa ta dawowa daga gonarsa da ke Budo Aare.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mota Mara Lamba Da Bindiga Kirar Pistol Da Kayan Maye A Kano 

Ɗan wanda aka sace, Abiola Owoade, ya shaida cewa maharan sun tare mahaifinsa tare da tafiya da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba. Ya ce a ranar Lahadi ne masu neman sa suka gano baburinsa a cikin wani daji, lamarin da ya ƙara tabbatar da cewa an yi garkuwa da shi.

A cewarsa, masu garkuwar sun tuntubi iyalan shugaban makarantar, inda suka nemi a biya su kuɗin fansa na naira miliyan 30 kafin su sake shi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo, CSP Olayinka Ayanlade, ya ce rundunar ta baza jami’anta tare da ƙaddamar da bincike domin ceto shugaban makarantar da kuma kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Advertisement

Ya ƙara da cewa rundunar na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an kuɓutar da wanda aka yi garkuwa da shi cikin ƙoshin lafiya, tare da gurfanar da masu hannu a lamarin a gaban doka.

 

 

PREMIUM TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending