Connect with us

Labarai

Ana shirin rantsar da zababbun ‘yan majalisar Somaliya a Mogadishu

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Muhammad muhammad Zahraddin

 

Ana shirin rantsar da wasu cikin sababbin ‘yan majalisar kasar Somaliya a yau Alhamis a cikin babban birnin kasar Mogadishu, bayan kammala zabukan da aka yi na tsawon watanni.

Za a rantsar da su cikin filin jirgin sama kasar – wanda wuri ne da yafi tsaro a fadin birnin – domin har yanzu ana fama da matsalar tsaro a kasar.

Majalisar kasar ta hada da majalisar wakilai mai mambobi 275, da kuma majalisar dattawa mai mambobi 54.

Babban aikin da ke gabansu shi ne na zaban shugaban kasar, wanda zai jagoranci wannan kasar a shekaru hudu masu zuwa.

Shugaba mai-ci Mohamed Abdullahi Farmajo ya ci gaba da rike mukami bayan karewar wa’adinsa saboda kauce wa matsalar siyasa a kasar, inda tun a watan Fabrairun bara wa’adin shugaba Farmajo ya kare

Advertisement

Shekara 30 ke nan da Somaliya ta shafe babu zaman lafiya, tun bayan da aka hambarar da gwamnatin marigayi Siad Barre a 1991, matakin da ya haifar da yakin basasa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending