Connect with us

News

Jami’an Kwastam Sun Kama Dabbobi Sama Da 40 Da Aka Yi Safarar Su Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano

Published

on

InCollage 20260827 213249401 scaled (1)

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce ta kama dabbobi da tsuntsaye 48 da ake zargin an yi safarar su ba bisa ka’ida ba a kan hanyar Kano zuwa Daura.

Jami’an shiyyar Kano da Jigawa ne suka gudanar da samamen a yammacin Talata, inda suka kuma kama wasu mutane uku da ake zargi da safarar namun daji, a cewar hukumar.

Yankuna 915 A Jihohi 19 Na Fuskantar barazanar ambaliyar ruwa — Gwamnatin Tarayya 

Daga cikin dabbobin da aka kama akwai caracal guda huɗu, chimpanzee guda huɗu, ƙananan birrai guda biyu, manyan birrai guda bakwai da galagos guda biyu.

Haka kuma, jami’an sun kwato honey badger guda ɗaya, albino alligators guda biyu, rock fowls guda shida, civet cat guda ɗaya da greater bustard birds guda 19.

Kwastam ta ce waɗanda ake zargin sun yi ƙoƙarin ba jami’an cin hanci domin su samu damar tsallake bincike, amma jami’an suka ƙi amincewa da tayin.

Advertisement

An miƙa waɗanda ake zargin da dabbobin da aka kama ga sashen kula da dabbobi da ke hedikwatar Kwastam domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin shari’a.

Hukumar ta ce kamen ya taimaka wajen dakile safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba, musamman dabbobin da ke fuskantar barazanar bacewa.

 

 

PRNIGERIA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending