News
Kotu Ta Tura Mutane 28 Gidan Gyaran Hali Bisa Laifin Dukan Jami’in Dan Sanda A Kano
Kotun Shari’ar Musulunci ta Ungogo, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muhammad Shurama, ta tura wasu mutane gidan gyaran hali bisa zargin haɗa baki wajen tayar da hankalin al’umma, jikkata jami’in ’yan sanda da kuma hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu.
Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Ɗan Kunkuru da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo, inda ake zargin wasu matasa da tayar da hargitsi.
Jami’an Kwastam Sun Kama Dabbobi Sama Da 40 Da Aka Yi Safarar Su Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
Bayan da ’yan sanda suka isa wurin domin shawo kan lamarin, an kama mutane 28, yayin da wani jami’in ’yan sanda ya samu rauni.
Kotun ta tura waɗanda ake zargin gidan gyaran hali, inda ta sanya ranar 1 ga watan gobe domin sake gabatar da su da ci gaba da sauraron shari’ar.
-
News4 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News2 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News3 days ago
Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 Ga Satumba A Matsayin Ranar Hutun Bikin Takutaha
