Connect with us

News

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Sayar Da Filin Sukuwa Kan Naira Miliyan 4.5

Published

on

IMG 7400

Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kama Tasiu Adamu Maje bisa zargin sayarwa da kuma bayar da hayar wani filin wasannin dawakai na gwamnati da ke Race Course, wanda aka fi sani da Filin Sukuwa.

Mukaddashiyar Shugabar hukumar, Hafsat Ada’u Kutama, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu.

“Babu Wata Kujerar Siyasa da Ta Kai Darajar Ran Dan Nijeriya” — Godswill Akpabio

Hukumar ta ce kama mutumin ya biyo bayan korafe-korafen da Muhammad Amir Yunusa da Usman Bala Yakasai (Sharif) suka shigar, inda suka zargi Maje da mika tare da bayar da kadarar ga wasu mutane masu zaman kansu ba tare da samun izinin da ya dace ba.

A cewar PCACC, binciken da ta gudanar ya nuna cewa Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, wadda ke da alhakin rabawa da kula da gidajen dawakai a jihar, ba ta san da wata mu’amala da aka yi da kadarar ba, kuma ba ta amince da ita ba.

Hukumar ta ce ta gayyaci tare da tattauna da wasu mutanen da ke da alaka da lamarin, inda ta gano cewa ba a taba ware gidan dawakai ga wani mutum a hukumance ba, ko ta hanyar sayarwa ko bayar da haya.

Advertisement

Haka kuma, PCACC ta ce takardar da ake zargin Maje ya yi amfani da ita wajen gudanar da mu’amalar ba takardar da Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta amince da ita ko ta san da ita ba ce.

Hukumar ta kara da cewa an yi zargin amfani da wannan takarda mara inganci wajen gudanar da mu’amala da mutane biyu daban-daban.

Binciken ya kuma nuna cewa ana zargin wanda ake zargin ya amince zai sayar da gidan dawakai ga Muhammad Amir Yunusa kan Naira miliyan 4.5, yayin da a lokaci guda yake karbar kudin haya daga Usman Bala Yakasai.

PCACC ta ce an nemi Yakasai ya biya Naira 180,000 a matsayin kudin haya, inda aka ruwaito cewa ya biya Naira 150,000.

Hukumar ta bayyana mu’amalolin da aka yi a matsayin bada izini ba, tana mai cewa gidan dawakai har yanzu mallakin gwamnatin Jihar Kano ne kuma yana karkashin kulawa da jagorancin Hukumar Wasanni ta jihar.

PCACC ta ce ta fara daukar matakan kwato kadarar tare da mayar da ita ga Hukumar Wasanni ta Jihar Kano.

Advertisement

Ana sa ran gurfanar da Maje a gaban kotun da ke da hurumin sauraron shari’ar, inda za a ba shi damar fuskantar tuhumar da ake masa bisa tsarin doka.

Hukumar ta gargadi jama’a da kada su shiga harkar saye ko hayar kadarorin gwamnati ba tare da tabbatar da mallakarsu da sahalewar hukumomin da abin ya shafa ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending