Connect with us

News

Kotu Ta Daure Wani Mutum Shekaru 10 Kan Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 11 A Jigawa 

Published

on

kotu 768x390 (1)

Babbar Kotun Jihar Jigawa da ke zamanta a Ringim ta yanke wa wani mutum mai shekaru 50, Abubakar Biniya, hukuncin daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali bayan ta same shi da laifin cin zarafin wata yarinya ’yar shekara 11.

‎Mai Shari’a Muhammad El-Usman ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan kotun ta tabbatar da cewa Biniya ya aikata laifin a watan Janairun 2024 a unguwar Galadanchi da ke Ƙaramar Hukumar Ringim.

‎An Kama Wani Mutum Kan Zargin Sayar Da Filin Sukuwa Kan Naira Miliyan 4.5

‎A yayin shari’ar, Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta gabatar da shaidu shida tare da wasu muhimman bayanai guda biyar, ciki har da rahoton likita, domin tabbatar da zargin da ake yi wa wanda ake tuhuma.

‎Biniya ya ba da shaida a gaban kotu a matsayin wanda ake tuhuma, amma bai gabatar da wani ƙarin shaida ba domin kare kansa.

‎Kafin yanke hukuncin, kotun ta ce ta yi la’akari da roƙon sassauci da Biniya ya yi, da kuma kasancewarsa wanda bai taɓa aikata laifi a baya ba.

Advertisement

‎Baya ga hukuncin daurin shekaru 10, Mai Shari’a El-Usman ya kuma umarce shi da ya biya yarinyar Naira 500,000 a matsayin diyya.

 

 

JUSTICE WATCH NEWS 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending