Connect with us

News

Musa Illiyasu Ya Jagoranci Sabon Kawance A Madobi Don Goyon Bayan Tinubu A 2027

Published

on

IMG 20260930 133409 127

Wasu jiga-jigan siyasa da magoya bayan jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Madobi ta Jihar Kano sun gudanar da wani taron nuna goyon baya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani yunƙuri na ƙara haɗa kan masu ruwa da tsaki a yankin gabanin zaɓen 2027.

Daya daga cikin jiga-jigan APC a Kano, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya jagoranta, ya samu halartar ɗaruruwan mata da matasa da sauran magoya bayan jam’iyyar.

Kotu Ta Daure Wani Mutum Shekaru 10 Kan Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 11 A Jigawa 

An gudanar da taron ne a Madobi, garin da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito, inda mahalarta suka rika rera taken nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu.

Da yake jawabi a wajen taron, Musa Illiyasu Kwankwaso ya ce an samar da sabon haɗin gwiwar siyasar ne domin ƙarfafa goyon bayan Shugaba Tinubu da kuma tunkarar zaɓen 2027.

Ya ce, “Madobi ba ta taɓa ganin irin wannan sauyin siyasa ba, domin a yanzu muna haɗa kai da mutanen da muka shafe shekaru 28 muna fafatawa da su a siyasa.”

Advertisement

Ya bayyana cewa a baya bangarorin biyu sun kasance suna fafatawa a zaɓe, inda wani lokaci ɗaya ke samun nasara, wani lokaci kuma ɗayan, amma yanzu sun yanke shawarar haɗa kai domin marawa Shugaba Tinubu baya.

Musa Illiyasu ya ce haɗin gwiwar ya haɗa da tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano kuma ɗan siyasar ƙasa, Habibu Hassan Elyakub, wanda ya ce sun daɗe suna fafatawa da shi a fagen siyasa.

A nasa jawabin, Elyakub ya ce haɗin gwiwar zai ƙara ƙarfi wajen tallata manufofin gwamnatin Tinubu a yankin.

Ya ce duk da cewa Kwankwaso ɗan asalin Madobi ne, Musa Illiyasu Kwankwaso ya ci gaba da samun nasarorin zaɓe a yankin, tun daga matsayin shugaban ƙaramar hukuma zuwa sauran mukaman siyasa.

“Saboda haka ba mu tsoron wannan haɗin gwiwa, kuma mun fito fili domin ganin Shugaba Tinubu ya samu nasara a zaɓen 2027,” in ji shi.

A nata jawabin, shugabar mata, Hajiya Assabe Diko, ta ce mata da matasa za su gudanar da kamfen daga gida zuwa gida domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin shiga harkokin siyasa da zaɓe.

Advertisement

Ta ce za su kai saƙon kamfen ga al’ummomi daban-daban domin ƙara yawan masu goyon bayan gwamnatin Tinubu.

A yayin taron, Musa Illiyasu Kwankwaso ya kuma bayyana wasu ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a Kano, ciki har da aikin babbar hanyar Abuja-Kaduna-Kano, ayyukan layin dogo, hanyoyin mota da kuma matakan inganta tsaro.

Ya ce ayyukan da gwamnatin ke aiwatarwa na daga cikin dalilan da ya sa suke ganin ya kamata a ci gaba da bai wa gwamnatin Tinubu goyon baya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending