Connect with us

News

YAN SANDA SUN KAMA WATA DILLALIYAR MIYAGUN KWAYOYI A KANO

Published

on

Daga mujahid danlami garba

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta kama wata dillaliyar miyagun kwayoyi mai suna Jamila Abdullahi mai shekaru 30 da haihuwa.

Wata majiya ta ce, Jamila Bazawara ce mazauniyar rukunin gidaje na Kwanar Ungogo da ke karamar hukumar Ungogo.

Advertisement

Jami’an tsaro dai sun samu bayanin cewa Jamila ce babbar dillaliyar shalisho a karamar hukumar Ungogo da kewaye.

Bayan ta shiga hannun ‘yan sanda, Jamila ta ce ita bazawara ce sannan ta dauki sama da shekaru biyu ta na saye da saida da shalisho, wanda ta ke sari a wurin wani mutum, amma bayan ya samu labarin ‘yan sanda sun kama ta sai ya gudu ya bar Nijeriya.

Advertisement

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifi irin wannan zai cigaba da gudanar da bincike kafin a kai Jamila kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending