News
Wasu gwagware a Birtaniya na yaudarar matan Ukraine
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Advertisements
Advertisements
Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewa maza masu cin zarafi na amfani da wani shiri na gwamnatin Biritaniya na karbar ‘yan gudun hijirar Ukraine don tuntubar ƴan mata masu rauni.
An gano cewa da yawa daga cikin mazan da gwagware ne na yin rijistar karbar ‘yan gudun hijira mata a karkashin shirin “ba da mafakar gida ga yan Ukraine”.
Binciken ya kuma gano cewa wasu ‘yan gudun hijirar sun rasa matsuguni a Burtaniya bayan da alaka tsakaninsu da masu masaukinsu ta ɓalɓalce.
Sai dai wani jami’in gwamnatin Birtaniya ya ce akwai matakan kariya da suka haɗa da na tsaro da kuma tantance bayanan duk masu ɗaukar nauyin ba da matsuguni kafin a ba wa baƙin biza.
Advertisements
Advertisements
