Labarai
MASU SHAYE SHAYE FIYE DA 500 SUN FECE DAGA GIDAN GYARAN HALI A SRI LANKA

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Daruruwan fursunoni ne suka tsere daga wata cibiyar gyaran hali ta masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a Sri Lanka bayan da suka lalata shingayen da aka sanya a wurin.
SAAUYA SHEKA: FUSATATTUN SANATOCIN AOC SUN GANA DA BUHARI A ASO ROCK
Tashin hankali ya barke ne bayan da ‘yan sanda suka shiga cibiyar gyaran halin ta Kandakadu don gudanar da bincike kan mutuwar guda daga cikin su.
Sanarwar da rundunar ‘yan sandan kasar ta fitar ta ce, fiye da rabin wadanda ke tsaren sun tsere a lokacin tarzomar sai dai an kai wani samame a yankin domin cafke su.
Bayanai sun nuna cewa ya zuwa ranar 16 ga watan Yuni, akwai mutane 951 da ake tsare da su a cibiyar karkashin umarnin kotu, bayan da aka same su da laifukan da suka shafi ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Hukumomin lafiya sun ce an samu karancin magunguna masu mahimmanci, ciki har da wadanda ake amfani da su wajen kula da masu matsalar shaye-shaye, saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar Sri Lanka.
Al’ummar tsibirin dai na fama da matsanancin rashin kudi sakamakon rashin kudaden ketare da ake amfani da su wajen biyan kudin abinci da man fetur da magunguna da sauran kayayyakin masarufi.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
