Business
Abu biyar da sabon rahoton hauhawar farashi a Najeriya ya kunsa.
Daga kabiru basiru fulatan
Wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na gurgunta tattalin arziki tare da karya darajar kuɗin da ke shiga hannun jama’a.
Shugaba Buhari ne ya hana daukar ma’aikata a Najeriya’-in ji ɗan majalisa
Wata hukumar hada-hadar kuɗaɗe da ƙimanta ƙarfin tattalin arzikin kasashen duniya ke da cibiya a Amurka mai suna Fitch Ratings ce ta fitar da rahoton ranar Alhamis.
Fitch Ratings ta ce hauhawar farashin na kawo naƙasu ga gudanar da hada-hadar kuɗi da kuma ci gaban kasuwanni a Najeriya.
Ga sauran abubuwan da rahoton ya ƙunsa da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe a Najeriyar.
1. Rahoton ya yi ƙiyasin cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa da kashi 3.1 a 2022, inda ake sa ran samun kuɗaɗe daga ɓangaren sayar da man fetur, haɗe da farfaɗo da harkoki bayan annobar korona.
Hukumar Fitch Ratings ta ce hakan zai taimaka wa wasu ɓangarori da ba na mai ba.
2. Tashin farashin kayayyakin zai yi wa tasirin cigaban dabaibayi tare da rage yawan abubuwan da jama’ar ƙasa ke iya saye da kuɗaɗen da ke shiga hannunsu.
3. Matakin da Babban Bankin Najeriya CBN ya ɗauka na ƙara yawan kuɗin ruwa a cikin watan Mayu, ba ya nuna wani sauyi na asali a tsarin hada-hadar kudi na kasar.
Hakan ya nuna cewa za a ci gaba da fuskantar matsala a ƙoƙarin farfaɗo da hauhawar farashin kayayyaki.
4. Har ila yau, rahoton ya yi hasashen cewa hauhawar farashi a Najeriya za ta ƙaru zuwa kashi 17 a 2022.
5. Duk da cewa Najeriya ta tsara cire tallafin mai kwata-kwata a bana amma ga alamu ba za ta iya cire shi ba har sai 2023, hakan ka iya taimakawa wajen daƙile hauhawar farashin.
Amma kuma ɗawainiyar biyan kuɗin tallafin man yana rage yawan kuɗaɗen da kamfanin man ƙasar NNPC ke zubawa a asusun gwamnatin.
Faɗa tsakanin Rasha da Ukraine dai, ya kara sanya hauhawar farashin kayayyaki a fadin duniya, musamman kayan abinci da makamashi da suka yi tashin ba a taba gani ba a wannan shekara.
