Business
Kasuwannin dabbobi na cigaba da samin masaya, duk da tsadar da dabbobi suke yi a kasuwanni.
Kasuwannin dabbobi na cigaba da samin masaya, duk da tsadar da dabbobi suke yi a kasuwanni.
Daga Sodiq Waya
Kasuwanin dabbobi na cigaba da samin masaya duk kuwa da tsadar da dabbobin ke yi a wannan shekarar.
Kamar yadda kowane abin amfani na yau da kullum ya ƙara kudi, dabbobi ma ba’a bar su a baya ba, domin kuwa za’a iya cewa kuɗin dabbobi ya ninka idan aka yi la’akari da yadda aka saye su a bara. Misalin ragon dubu 50 a bara, a bana sai ya kai kusan dubu 100.
A ziyarar da na kai kasuwanin dabbobi da ke cikin birnin Kano, masu sayar da dabbobin sun koka sosai akan yadda aka sami hauhawar farashi wacce ba’a taɓa samin irinta ba a tarihi.
Malam Audu Mayau, dattijo ne da ke sana’ar sayar da dabbobi a kasuwar Garu da ke ƙaramar hukumar Madobi ya bayyanawa Jaridar Daily Enquirer cewa: “Tsadar dabbobin da ake fuskanta bana na da alaƙa da tashin farashin man dizel wanda manyan motoci suke amfani da shi domin ɗebo dabbobin daga inda aka sayo su da kuma shi kansa abincin dabbobin.”
Wani mai sana’ar sayar da dabbobi a wata kasuwa da ke kusa da Kofar Dawanau mai suna Mahmoud Saniya, ya bayyanawa gidan jaridar Daily Enquirer cewa “Tsadar da dabbobi suke yi bai hana mutane sayan dabbobin ba, domin kuwa kusan kullum yana sayar da dabbobi sama da 10.
Rahotanni daga sassan ƙasar nan sun yi nuni da yadda tsadar dabbobi ke cigaba da ta’azzara.
Fatan mu dai a nan shi ne Allah Ya horewa musulmi abinda za su saya na layya.
