News
Ƴan adaidaita sahu za su tsunduma yajin aiki a Kano
Matuka babauran adaidaita sahu a jihar Kano za su tsunduma yajin aiki.
Matakin na su ya biyo bayan ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana da suke yi bisa umarnin sauya lamba da hukumar KAROTA ta ba su.
Ka a yammacin ranar Alhamis
Zanga-zangar dai ta biyo bayan yadda hukumar KAROTAR ta ce sai sun biya kudi Naira dubu takwas domin sabunta lambar ta su.
Sun kuma koka kan yadda KAROTA ke karbar kudaden haraji barkatai a hannun su musamman ma na ranar lahadi da ba sa fita aiki.
Matuka baburan sun bayyana cewa daga lokacin da hukumar KAROTA ta fara kamasu su ma za su tafi yajin aiki.å