News
An kashe ‘yan bindiga 38 a Katsina
An kashe akalla ‘yan bindiga 38 yayin da ‘yan sanda biyar suka mutu a samame daban-daban da aka kai cikin jihar Katsina.
Rundunar ‘yan sanda jihar Katsina ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana karkashin shugaban ‘yan sandan jihar Sanusi Buba.
“Babu shakka wannan shekarar da ta kare an fuskanci kalubale mai yawa a Katsina musamman na tsaro, sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasarori masu yawa a yakin da take da ‘yan bindiga da masu satar mutane da ‘yan fashi da sauran manyan laifuka da ake aikatawa.
Duk da haka 2021 cikinta an samu raguwar wadannan laifuka idan aka kwatanta da 2020″.
“Cikin rikicin an samu nasarar kashe ‘yan bindiga 38 an kuma kashe mana jami’ai 5.”
Rundunar ta ce an kama wasu da ake zargi da muggan ayyuka 999 da suke da alaka da manyan laifuka 608.
A gefe daya kuma an kama wasu mutum 874 na daban da aka gurfanar gaban shari’a a jihar.