Connect with us

News

Mun Hallaka ’Yan Ta’adda Sama Da 1,000 A 2021 – Gwamnatin Tarayya

Published

on

Lai Mohd
Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta ce yakin da take yi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas na samun gagarumar nasara, inda dakarunta suka samu hallaka ’yan ta’adda sama da 1,000 a shekarar 2021 mai karewa. Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a Legas, yayin wani taron manema labarai ranar Alhamis.A cewarsa, yayin da ’yan ta’adda kimanin 22,000 suka mika wuya, an kuma samu ceto fararen hula 2,000 tare da kwato makamai masu yawa da kuma tarwatsa masana’antun kera bama-bamai daga kungiyoyin ISWAP da Boko Haram.Sai dai Ministan ya amince cewa babban kalubalen da gwamnati mai ci ke fuskanta shi ne na matsalar tsaro.Amma ya ce duk da wadannan kalubalen, sojoji sun taka rawar gani.“A shekarar nan mai karewa, babban kalubalenmu shi ne na rashin tsaro. Sai dai duk da hakan da kuma kalubalen tattalin arziki, gwamnati mai ci ta taka rawar gani, kuma ta cancanci yabo.“Jama’a, rundunarmu da ke Arewa maso Gabas karkashin Operation Hadin Kai, gta sami nasarar hallaka ’yan ta’adda sama da 1,000, ’yan ta’adda da iyalansu sama da 22,000 sun mika wuya ga sojoji, yayin da aka ceto fararen hula 2,000.”Lai Mohammed ya kuma ce a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya, Rundunar Sojin kasar nan ta kafa sansanoni daban-daban a sassa da dama na kasar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *