Connect with us

Business

Ilimin Fasahar Zamani: NITDA ta horas da ƴan ƙasa 120,000

Published

on

FB IMG 16409698834278692
Spread the love
Hukumar Ci gaban Fasahar Zamani ta Ƙasa, NITDA ta ce ta horar da ƴan Nijeriya 120,000 a faɗin ƙasar nan a kan Ilimin Fasahar Zamani.
Darakta-Janar na hukumar, Kashifu Inuwa ne ya baiyana haka a yau Juma’a a yayin da ya ke jawabi a ƙarshen wata horas wa ta kwana 3 da a ka yi wa ƴan jarida da ga arewa-Maso-Yammacin Nijeriya a cibiyar PRNigeria a Kano.
A cewar sa, hukumar na faɗaɗa Ilimin Fasahar Zamani har ya zama cewa kashi 95 na ƴan ƙasa zuwa shekarar 2030.
Kashifu ya ƙara da cewa Hukumar da ta cimma wannan ƙuduri ne ta hanyar shirye-shirye iri-iri da su ka haɗa da Cibiyar Koyar da Fasahar Zamani, Shirin Fasahar Zamani na Jihohi, da sauran su.
“Mu na kuma aiki tare da wasu ƙungiyoyi ingantattu da za su taimaka mana wajen horaswar sabo da gwamnati ba za ta iya ita kaɗai ba.
  1. “Hakan ne ma ya sanya mu ka sanya ƴan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin cimma wannan buƙatar,” inji shi.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *