Shugaba Buhari ya ce abin da ya faru a baya ya wuce, amma alherin da ke gaba yana da darajar gaske.
A wani rubutaccen sakon shugaban Najeriya na shiga sabuwar shekara ta 2022, ya bayyana damuwa ainun game da tabarbarewar tsaro inda ya mika ta’aziyarsa ga ‘yan uwa da iyalan jami’an tsaro da fararen hular da suka rasa rayukansu sanadiyar rashin zaman lafiya.
Shugaba Buhari, wanda ya ce ya samar da kayan aiki da sake salon rundunonin tsaro don kare rayuka da dukiyar al’umma, ya nuna gwamnatinsa ba za ta yi kasa a guiwa ba, don tunkarar lamuran tsaro daje kan gaba a lamuran da ya fi maida hankali a kai.
Haka kuma shugaban ya jinjinawa Majalisar Dokoki don amincewa da dokar sashen Man Fetur PIB a takaice, da ta yi garambawul ga sashen, ya na mai cewa a bana gwamnatin sa za ta kara maida hankali kan kimiyyar yanar gizo wajen fadada hanyoyin tattalin arziki.
Ga shugaban matasa na tsohuwar jam’iyyar CPC da shugaba Buhari ya kafa Abubakar Maikudi, duk abun da shugaban ya aiwatar in dai ba ya bin sawu ba za a samu tasiri ba.
Shi kuma jigo a kamfen din shugaban Aminu Madaucin Bakori, ya aza alhakin wasu matakan da ke jawowa shugaban suka da rashin tasiri kan mukarrabai.
Shugaban dai zai share shekarar da bin kasafin kudi na Naira tiriliyan 17.1, ya yi korafi kan yanda ‘yan Majalisa su ka cusa aiyuka 6,576 a ciki,
Hakan na nuna kusan kowane dan Majalisa zai tashi da kimanin aiyuka 14 kasancewar yawan dukkan ‘yan Majalisar 469.