Farmakin ya yi sanadiyyar kashe wasu manyan kwamandojin yan bindigar a ya yin kuma da suke jana’iza, haka kuma sojojin saman sun kara afkawa ‘yan bindigar inda aka kara kashe karin wasu gomman yan bindigar.
Bayanai dai sun tabbatar da jiragen yakin Najeriyar sun kashe wasu manyan yan bindigar da ba a bayyana sunansu ba kawo yanzu. Kodayake wata majiya ta tabbatarwa wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, cewa wani jami’i a hedkwatar tsaron kasar ya tabbatar da wannan labari yana mai cewa nan gaba kadan za suyi taron manema labarai akan batun.