Connect with us

News

An gano jaririn da aka jefar a bandakin cikin jirgi

Published

on

2414666d 6eee 49a3 a04b 0a64e6e63e57

Daga yasir sani abdullahi

Ma’aikatan filin jirgin saman Mauritius sun gano wani jariri sabon haihuwa da aka jefar da shi a cikin sharar da ke ban-dakin cikin jirgi.

Advertisement

An tsare wata mace mai shekara 20 ‘yar kasar Madagascar, wadda aka yi zargi ta haifi jaririn a cikin jirgin.

Jirgin na kamfanin Air Mauritius, wanda ya isa kasar daga Madagascar, ya sauka a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Sir Seewoosagur Ramgoolam International ranar 1 ga watan Janairu.

Advertisement

Ma’aikatan jirgin sun gano jaririn ne lokacin da suke bduba jirgin kamar yadda ake yi a ko da yaushe.

Daga nan suka garzaya da jaririn asibiti domin a kula da lafiyarsa.

Advertisement

Matar da ake zargi da haihuwar jaririn, wadda da farko ta musanta haihuwarsa, an gudanar da gwaje-gwaje a kanta wadanda suka tabbatar da cewa ita ta haife shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending