Connect with us

News

Dole a hukunta Trump bisa kisan Soleimani – Raisi

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya ce dole a hukunta tsohon shugaban Amurka Donald Trump bisa kisan babban janar din sojin kasar Qassem Soleimani shekaru biyu da suka wuce, idan ba haka Iran za ta yi ramuwar gayya.

A wani jawabi da ya gabatar ta gidan talbijin ranar Litinin, shugaban shugaban kasar ta Iran ya ce “babban mai laifi kuma makashi” wanda ya bayar da umarnin kai hari da jirgi maras matuki a kan jerin gwanon motocin Soleimani a Iraq, Trump dole ne ya fuskanci “shari’ar Allah” sannan ya fuskanci “qisas”, wanda a Musulunce yake nufin ramuwar gayya.

Raisi ya yi kira a kafa “kotun adalci” wadda Trump, da tsohon Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo da sauran jami’an kasar za su gurfana a gabanta sannan a hukunta su.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *