Rundunar ‘yan sandan Jamhuriyar Nijar ta kama hodar cocaine mai nauyin fiye da kilogiram 200 wadda kudinta ya kusa $8.7m a cikin motar wani magajin gari, a cewar wasu majiyoyin ‘yan sanda.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, wanda ya rawaito wannan labari ranar Litinin, ya kara da cewa an kama magajin garin da direbansa, wadanda suke cikin motar, da kulli 199 na hodar cocaine a wani wajen binciken ababen hawa da ke wajen birnin Agadez ranar Lahadi.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin da ke yaki da miyagun kwayoyi na kasar ya tabbatar da kama fiye da kilogiram 200 na cocaine a Agadez, kodayake bai yi karin bayani ba.
Wasu kasashen Yammacin Afirka sun kasance hanyar da ake bi wajen safarar miyagun kwayoyi daga Kudancin Amurka zuwa Turai, kuma a ‘yan shekarun nan an samu karuwar kama miyagun kwayoyi a yankin.