Connect with us

News

kamfanonin sadarwa su dakatar da aikin fasahar 5G

Published

on

Spread the love

Daga kabiru Basiru Fulatan

 

Hukumomin Amurka sun nemi kamfanonin sadarwa na AT&T da Verizon da su jinkirta aikin sadarwar 5G har tsawon makonni biyu, yayin da ake ganin rashin tabbas game da katsalandan ga mahimman kayayyakin kariya na jirgen sama.

Tuni dai kamfanonin suaka fitar da sanarwar cewa sun fara nazartar wannan bukata ta gwamnatin Amurka.

Advertisement

A ranar 5 ga watan Disamba ne Amurka ta fitar da fasahar sadarwar wayar tafi da gidanka, amma aka jinkirta zuwa ranar 5 ga watan Janairu bayan da manyan kamfanonin sararin samaniyar Airbus da Boeing suka nuna damuwa game da katsalandan da na’urorin da jiragen ke amfani da su wajen auna sahihancin shirin.

Sakataren Sufuri na Amurka Pete Buttigieg da Shugaban Hukumar Kula da Jiragen Sama, Steve Dickson, sun nemi jinkirin baya-bayan nan a cikin wata wasika da aka aika ranar Juma’a ga AT&T da Verizon, manyan manyan kamfanonin sadarwa na kasar.

A cikin wasikar, hukumomin Amurka sun ba wa kamfanonin tabbacin cewa sabis na 5G zai iya farawa kamar yadda aka tsara a watan Janairu sai dai akwai bukatar a bawa wasu filayen jiragen sama masu muhimmanci damar da suke bukata.

Advertisement

Hukumomin kasar dai sun ce akwai bukatar kare lafiyar jiragen sama, tare da tabbatar da cewa tura 5G da ayyukan jiragen sama na iya kasancewa tare.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *