News
ECOWAS Jam’iyyun siyasa sun yi watsi da shirin sojin Mali

Babbar gamayyar jam’iyyun siyasar Mali ta yi watsi da shirin gwamnatin sojin kasar na mika mulki ga farar hula nan da shekaru biyar masu zuwa.
Ministan Harkokin Wajen Mali, Abdoulaye Diop ya gabatar da sabon shirin sojojin ga Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS a ranar Asabar da ta gabata, bayan gudanar da wani taron-gyaran-kasa wanda jam’iyyun siyasar da na ci gaban al’umma suka kaurace masa.
Shirin dai ya kunshi cewa, sai an shafe tsawon shekaru biyar sojojin na gudanar da mulkin rikon kwarya kafin daga bisani su mika ragamar kasar ga farar hula, kuma daga 1 ga wanann wata na Janairu, aka fara lissafin tsawon wa’adin na shekaru biyar.
Gamayyar Jam’iyyun ta ce, wannan sabon tsarin jadawalin ya yi karan-tsaye ga yarjejeniyar mika mulkin, inda kuma ta ce, ya yi hannun riga da muradun ‘yan kasar ta Mali.
A cikin sanarwar da ta fitar, gamayyar ta ce, ta yi watsi da wannan jadawalin wanda ta ce, wani bangare ne kawai ya yi gaban kansa wajen amincewa da shi.
A ranar 9 ga watan nan na Janairu ne, Kungiyar ECOWAS za ta gudanar da wani taro kan batun na Mali a babban birnin Accra na Ghana.