News
‘Yan sanda sun kubutar da almajiran da aka sace a Zamfara
Dag Usman Abdullahi Nguru
Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara da ke arewao maso yammacin Najeriya ta ce ta miƙa wasu ƙananan yara 21 da ta kuɓutar, bayan mahaifansu sun tura su zuwa karatun Islamiyya amma ‘yan fashin daji suka tare motarsu cikin dare a ƙarshen mako.
Ta ce ƙananan yaran sun fito ne daga ƙaramar hukumar Bakura a kan hanyarsu ta zuwa Ɗan Dume cikin jihar Katsina mai maƙwabtaka, kafin sace su a ranar Juma’a.
Alƙaluma sun nuna cewa an sace ɗalibai sama da 1000 a cikin shekarar da ta yi bankwana akasari a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Neja.Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya fada wa BBC cewa ranar Juma’a daliban su 19 da mata biyu “sun kawo daidai dajin Kucheri ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su.”
Ya kara da cewa wasu mutane ne suka tsegunta wa hadakar jami’an tsaron yankin inda barayin suka ajiye yaran kuma nan da nan suka tunkare su suka kwato yaran.
SP Muhammad Shehu ya kuma tabbatar da cewa babu ko da yaro daya daga cikinsu da ya samu rauni ko wata matsala yayin artabun, kuma an kubutar da su duka.
Da BBC ta tambaye shi halin da suke ciki sai ya ce “suna cikin koshin lafiya domin an duba lafiyarsu babu wani wanda ke cikin wani yanayi na rashin lafiya.”