Connect with us

News

Bashir Tofa Cikakken Dan Dimokradiyya Ne Mai Kishin Kasa – Atiku

Published

on

1FE4F716 CA86 460F 99D7 8DA9F283C0B3 w408 r1
Spread the love

 

Daga Muhammad zahraddin Muhammad

“Tabbas wannan babban rashi ne. Ina Addu’ar Ubangiji Allah ya jikansa ya yafe masa. Allah ya ba shi gidan Aljanna. Ameen.” In ji Atiku

Advertisement

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya kwatanta rasuwar tsohon dan takarar shugaban kasa Alhaji Bashir Tofa a matsayin babban rashi.

Da safiyar Litinin Bashir Tofa ya rasu bayan fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya a Kano.

Tuni dai an yi jana’izar marigayin a ranar Litinin a birnin na Kano.

Advertisement

“Marigayi Bashir Tofa cikakken dan Dimokuradiyya ne da kishin kasa. A kowanne lokaci yakan ba da gudunmowa da shawara akan al’umara da suka shafi wannan kasa.” Atiku ya ce cikin sanarwar.

“Tabbas wannan babban rashi ne. Ina Addu’ar Ubangiji Allah ya jikansa ya yafe masa. Allah ya ba shi gidan Aljanna. Ameen.” In ji Atiku.

Mariyagin ya tsaya takarar shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar NRC a 1993 inda ya kara da dan takarar SDP MKO Abiola.

Advertisement

Abiola ya lashe zaben, amma gwamnatin mulkin soji karkashin Janar Ibrahim Babangida ta soke zaben.

‘Yan Najeriya da dama sun yi ittikafakin cewa zaben shi ne mafi sahihanci da kasar ta taba yi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *