News
Kotu ta ɗaure matashi a gidan yari sakamakon satar talo-talo a Kano

Daga kabiru basiru fulatan
Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 23, Nura Usman, hukuncin daurin watanni biyu a gidan ajiya da gyaran hali, bisa samunsa da laifin satar talo-talo.
Usman, wanda mazaunin unguwar Rimin Kebe Quarters ne a Kano, an yanke masa hukuncin ne bayan ya amsa laifin sata.
Alkalin kotun, Mansur Ibrahim, ya kuma ba shi zabin biyan tarar Naira 20,000 tare da umarce shi da ya biya Naira 16,000 a matsayin diyya ga mai talo-talon.
Tun da farko, dai Lauyan masu shigar da kara, Abdullahi Muhammad ya shaida wa kotun cewa, wanda a ke tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Janairu, a unguwar Rimin Kebe da ke Kano.
Ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa kai cikin gidan wanda ya kai karar inda ya saci Talo-Talo daya. Sai dai wanda a ka yanke wa hukuncin ya sayar da talo-talon ne a kan kudi Naira 7,000.
Lauyan ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 133 na dokar shari’ar jihar Kano.