Connect with us

News

Mutuwar Bashir Tofa babbar asara ce ga Najeriya — PDP

Published

on

FB IMG 16409937713379550
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

Jam’iyar adawa ta PDP ta baiyana rasuwar Bashir Othman Tofa a matsayin babbar asara ga Nijeriya.

Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu ne ya baiyana haka a wani saƙo da ya fitar na ta’aziyyar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar NRC.

Advertisement

Ayu ya nuna kaɗuuwa da jimami dangane da rasuwar marigayi Bashir Tofa, in da ya baiyana cewar, “ba shakka ƴan Nijeriya sun yi rashin adilin ɗan siyasa mai hangen nesa da son cigaba.

“Bashir Tofa dattijo ne a kalamansa da huldarsa, nayi hasara abokin shawara, mutum mai hikima da raha tare da maraba a tsakaninmu don sadar da sakon da zai amfani al’umma cikin adalci da gaskiya ga kowane bangare na kasarnan” In ji Ayu.

Ya ce ” al’ummar Jihar Kano da na Arewa da ma ƙasa baki ɗaya su sanya iyalai da ƴan uwan marigayin cikin addu’oinsu sakamakon wannan rashin mai girma na dattijo, jarumi, ɗan kishin ƙasa, mutum mai taimakon al’umma da tsare gaskiya a zantukansa da hulda da kowa, mussaman daga cikin yan siyasa Nijeriya.”

Advertisement

Dakta Ayu ya baiyana Marigayi Tofa da kasancewa namijin duniya da ba shi da fargaba ga baiyana abin da ya dace da aikata hakan gaban kowa don ciyar da al’ummarsa da ƙasarsa a gaba, tare da neman haɗin kai.

Baya ga gabatar da ta’azziyarsa ga iyalai da sauran ƴan uwa da masoya al’umma Nijeriya, Ayu ya kira tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Alhaji Umar Ghali Na’abba don sadar da sakon ta’azziya da rokon Allah Ya gafarta masa da mafificin alherinsa da rahama a kabarinsa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *