News
2023: Ina da yawan magoya bayan da zan iya cin zaɓen shugaban ƙasa — Kwankwaso
Daga Muhammad zahraddin
Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso ya ce yana da ɗumbin magoya baya a ƙasar nan da za su ishe shi ya ci zaɓen shugaban ƙasa a 2023 idan har ya yanke shawarar tsayawa takara.
Kwankwaso, tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, ya baiyana hakan ne a wata hira da ya yi da Gidan Rediyon DW Hausa a Abuja a jiya Laraba.
Kwankwaso ya ce yana nan dai ya fara tuntuba a kan ko ya tsaya takarar shugaban ƙasa, inda ya ce zai sanar da matsayar da nan ba da daɗewa ba.
“A wannan yanayi da a ke ciki, ba gaggawa mu ke yi ba.
“Mu na dai yin nazari kuma mu na tuntuɓar mutanen da su ka dace domin su bamu shawara. Duk abinda na yanke, to jama’a za su ji da ga gare ni.
“Mu ma da magoya bayan da sun ishe mu samun nasara a kowacce irin takara mu ka tsaya.
“Mu na da magoya baya a ko ina, ba wai a Nijeriya kaɗai ba, har ma a kasashen waje. Mutane sun za ci magoya bayan mu a Kano ko Arewa kawai su ke, amma magana ta gaskiya, mu ma da magoya baya a Nahiyar Asiya, Amurka da Nahiyar Turai,” in ji Kwankwaso.