Hukumar rubuta jarrabawar shuga manyan makarantu ta kasa JAMB ta ce har yanzu bata fara siyar da fom din rubuta jarrabawar ba na bana.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, inda ta gargadi dalibai da su kula don kaucewa fadawa komar bata gari.
Hakan na zuwa ne bayan da hukumar ta samu rahotannin sirri na wasu mutane dake amfani da sunan hukumar wajen bayyana cewar an fara rajistar ta shekarar 2022.
Hukumar ta kuma kara da cewa zata sanar da daukacin dalibai da sauran al’umma masu muradin yin rajistar a bana ta kafafan yada labarai kamar yadda aka saba.