Rundunar sojin kasar nan ta rufe kasuwar shanu ta garin Song dake jihar Adamawa, bayan samun bayanan sirri cewar ‘yan Boko Haram ne ke cin kasuwar.
Rufe kasuwar dai ya janyo cece-kuce daga bangaren ‘yan kasuwa da ke sukar matakin da rundunar sojin ta dauka.
- Matsalar Tsaro: Kimanin mutum 10, 400 suka rasu a shekarar 2021 a Najeriya
- Gwamnatin jihar Jigawa ta biya Naira 9.403bn ga wanda sukai ritaya a shekarar 2021
Wani dan kasuwa da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya shaidawa jaridar PUNCH cewar jami’an sojin sun bukaci milyoyin Nairori daga wajen ‘yan kasuwar kafin daukar wannan matakin.
Sai dai Kwamandan rundunar soji dake aiki a yankin Brigadiya Janar Aminu Garba na cewa, an rufe kasuwar ne na wucin gadi don tsaida ayyukan ‘yan ta’adda.
“Hakan ya zama wajibi duba da cewa, ‘yan ta’adda na amfani da kasuwar wajen siyar da shanun sata.”
A gefe guda kuwa, Hakimin garin Song Alhaji Ahmadu Sa’idu, ya shaidawa manema labarai bai da masaniyar rufe kasuwar da jami’an soji suka yi a baya-bayan nan, wanda bayanai ke nuni da cewa don sun ki basu hadin kai ne.
“Sun sanar da ni cewar matakin na su na da alaka da bincike na tsaro da suke son aiwatarwa a kasuwar,” Alhaji Ahmadu Sa’idu.
Idan ba a manta ba dai, sojoji sun rufe wata kasuwa a garin Gombi wadda ake da bayanan ‘yan tada kayar baya za su kai hari.
Gombi dake kusa da tsaunin Mandara, ‘yan tada kayar baya ke amfani da shi wajen fakewa don kai hare-hare ga mutanen dake karamar hukumar Askira Uba cikin jihar Borno, sai Michika da Madagali da Hong su kuma cikin jihar Adamawa.