Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya ta kara harajin N10 kan lemon kwalba

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad zahraddin

Gwamnatin Najeriya ta ƙara harajin naira 10 kan duk wata lita da duka lemukan kwalba da ba giya ba, da sauran wasu lkayayyakin kwalama.

Wannan sabuwar dokar ma dauke ne cikin dokar kudi ta gwamnati ta 2021.

A cewar dokar an sanya wannan haraji ne domin rage yawan shan sikari wanda yake janyo ciwon siga da kuma kiba, da dai wasu abubuwan na daban.

Advertisement

Ministar kudi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce an samar da wannan karin kudin ne kan abubuwan da ke janyo rashin lafiya da kashe kudade ba bisa dalili ba.

Cikin kayayyakin da abubuwan suka shafa akwai Coca-Cola, Pepsi, Sprite da sauran abubuwan da suke janyo kiba saboda zakin da suke da shi.

Rahotanni sun ce akwai kimanin ;’yan Najeriya miliyan hudu da ke fama da ciwon siga wanda ke da alaka kai tsaye da yawan shan siga da suke yi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *