Connect with us

News

2023: APC ta sulhunta Goje da gwamnan Gombe, Y

Published

on

FB IMG 16414679088589864
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

Kwamitin Shugabacin Jam’iyar APC na Wucin-gadi, ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni ya sulhunta tsakanin Gwamna Muhammad Yahaya na Jihar Gombe da kuma abokin burmin sa na siyasa, tsohon gwamnan jihar, Sanata Ɗanjuma Goje.

Jami’in Yaɗa Labarai na Buni, Mamman Mohammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba a Abuja.

Advertisement

Ya ce Buni, da Shugaban Kwamitin Sulhu na APC, Sanata Abdullahi Adamu da Kashim Shattima, mamba a kwamitin, su su ka jagoranci sulhun.

Sanarwar ta ce wannan shine karon farko da manyan ƴan siyasar na Gombe su ka haɗu tun bayan da rigimar siyasa ta ɓarke tsakanin su a shekarar bara.

Buni, wanda shine kuma Gwamnan Jihar Yobe, ya baiyana jin daɗin sa game da sulhun da a ka yi.

Advertisement

Ya kuma ci alwashin sulhunta duk masu ruwa da tsaki a APC domin ƙarfafa jam’iyar yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *