Connect with us

News

Hukumar KAROTA Ta Shirya Tsaf Don Fara Kaman Masu Adaidaita Sahu

Published

on

FB IMG 16415101074496124
Spread the love

 

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin

 

Advertisement

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA tace zata fara cafke masu tuka baburan adaidaita sahu da suka ki sabunta takardun izinin tukin su.

Manajan Daraktan hukumar, Baffa Babba Dan-Agundi, shine wanda ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan hukumar na shekarar 2021, ya ce matakin zai zama abin tunatarwa ga mahaya da suka kasa sabunta takardar izinin.

“Wadanda suka kasance wannan shine karon su na farko wajen samun takardar izinin za su biya naira 18,000, yayin da wadanda suka sabunta ta za su biya naira 8,000 kacal,” in ji Dan-Agundi, inda ya kara da cewa a hukumance ranar da za a fara kama su a ranar 1 ga watan Janairu sabuwar shekarar 2022.

Advertisement

Baffa ya kuma ce hukumar ta hada hannu da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar domin kamo direbobin wadanda basu da abin kayyadewa motocinsu ma’aunin gudu ba tare da mika su ga hukumar domin daukar matakin da ya dace.

Sannan yace: “A cikin sabbin tsare-tsarenmu na shekarar 2022, jami’an KAROTA zasu fara damke duk direbobin da ba su da mitar da ke kayade gudun ababen hawa tare da mika su ga hukumar FRSC.

Kazalika Dan-Agundi ya kuma ce hukumar ta dauki sabbin ma’aikata 1,000 a shekarar 2021 tare da kara motocin aiki daga uku zuwa 60, da kuma sabbin mashina tsere guda 50.

Advertisement

Ya kuma ce a cikin shekarar da mukayi ban kwana da ita a binciken da aka gudanar jami’an hukumar sun kama barayi wadanda suka yi amfani da babura masu kafa uku wurin satar yara, da kwace wayoyi da sauran laifuffuka kuma yawancinsu an kai su kotu.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *