Sojojin Najeriya sun ‘kashe Alhaji Auta da ‘yan ta’adda 950’ cikin wata bakwai
Sojojin Najeriya
Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ta kashe waɗanda ta kira ‘yan ta’adda 950, ciki har da shugabannin ‘yan fashin daji Alhaji Auta da Kacalla Ruga cikin wata bakwai da suka gabata.
Muƙaddashin shugaban sashen hulɗa da jama’a na sojin Najeriya, Manjo Janar Bernard Onyeku, ya faɗa a yau Alhamis cewa sun samu nasarar ce tsakanin 20 ga watan Mayun 2021 zuwa 6 ga Janairun 2022.
Game da kisan jagororin ‘yan fashi, Janar Onyeku ya ce: “An samu nasarar a ranar 3 ga watan Janairun 2022 bayan samun bayanan sirri da ya bayyana wuraren ɓuyan shugabannin ‘yan fashi biyu Alhaji Auta da Kacalla Ruga…’Yan fashi kusan 100 aka kashe yayin fafatawar.”
Cikin lokacin da ake magana, rundunar Hadarin Daji ta kashe jumillar ‘yan fashin daji 537 tare da kama 374. Bugu da ƙari rundunar ta ceto mutanen da aka yi garkuwa da su kusan 1,000.
Kazalika, dakaru sun ƙwace makamai 227 da kuma harsasai iri daban-daban 4,443. Haka nan an ƙwato dabbobi 3,250 da aka sata a lokacin.