News
An yi wa turawan da suka kashe Ahmaud Arbery ɗaurin rai-da-rai Mintu
Daga Yasir sani Abdullah
Wata kotu a Amurka ta sami wani uba da dansa da laifin kashe wani bakar fata yayin da yake gudun motsa jiki.
Kotun ta sami Travis da dansa Gregory McMichael da wani makwabcinsu William Bryan da laifin kashe Ahmaud Arbery saboda kawai shi bakar fata ne a watan Fabrairun 2020.
Dukkan mutanen, wadanda turawa ne za su shafe sauran kwanakin da suka rage mu su a gidan kurkuku, sai dai mutum na uku na iya neman a sako shi bayan shekara talatin
Kamar dai shari’ar nan da aka yi wa dan sanda Derek Chauvin wanda ya kashe bakar fatan nan George Floyd, wannan shari’ar ma ta ja hankalin duniya.