News
Me ya sa mutane da dama ke rububin zuwa Duniyar Wata a 2022?
Daga Muhammad zahraddin
A shekarar nan ta 2022, kasashe, kamfanoni da kungiyoyi za su yi ta rige-rigen tafiya duniyar wata. Tuni shirin Artemis na Hukumar Kula da Sararin Samaniya mai zaman kanta ta Amurka NASA ta fara shirin tabbatar da an samu mutane da dama a can duniyar watan zuwa shekarar 2025. Wadanne abubuwa ne suke faruwa a can duniyar a bana, kuma mene ne burin masu niyyar zuwan?
Bana za a yi ta gogoriyon zuwa duniyar wata, bayan a bara ba samu ko mutum daya da ya sauka a duniyar ba.
Hukumar NASA za ta kaddamar da shirinta na Artemis, sannan za ta dauki nauyin masu burin zuwa domin kai kayayyakin aiki da sauran abubuwan da masu binciken sararin samaniya za su bukata domin gudanar da bincikensu a nan gaba.
Kasashen India da Japan da Rasha da Koriya ta Kudu da Hadaddiyar Daular Larabawa ma za su kaddamar da shirinsu na zuwa duniyar watan a bana, haka ma akwai kamfanoni da dama da suke da burin haka duk a banan.
Duk tafiye-tafiyen nan za a yi su ne da jiragen da babu matuka, kuma su ne za su zama kamar sharar fage domin tabbatar da kasancewar mutane a duniyar wata a nan da kasa da shekara 10.
Duk da cewa ba shi ba ne babban burinsu-assasa tashar sauka da tashin jirage a duniyar watan yana cikin shirye-shiryen tafiya har zuwa duniyar Mars.
Dokta Zoë Leinhardt, masanin sararin samaniya ne a Jami’ar Bristol da yake da tunanin cewa a bana za a samu wani cigaba na rige-rigen zuwa duniyar wata har da wasu kasashen da ba su damu da bangaren ba a baya.
Kasashe da dama da suke da burin zuwa duniyar watan, za su je ne domin gudanar da bincike, amma wasu suna da wata babbar manufar.
“Wasu matafiyan suna da dadadden burin zuwa duniyar watan domin tabbatar da shirinsu da kuma gwada sababbin fasaharsu da kuma wasu hadakan gwiwa da suka shiga,” inji Dokta Leinhardt.
To wadanne shirye-shiryen tafiya ne a kasa, kuma mene ne manufofin kowanne daga cikinsu: