Connect with us

News

Mijina na neman kashe ni da yawan jima’i, mata mai neman saki ta shaidawa kotu

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Wata mata mai ƴaƴa 3, Olamide Lawal, a ranar Juma’a ta roƙi wata kotun gargajiya mai matakin A a Mapo, Ibadan da ta kashe auren ta a bisa dalilin cewa mijinta, Saheed Lawal, ya na yin jima’i da ita har ya wuce kima.

A ƙarar da Olamide ta shigar, ta kuma shaidawa kotun cewa mijin nata ɗan giya ne.

“Shekarar mu 14 kenan da aure na da Lawal. Ɗan giya ne da bashi da niyyar denawa kuma bashi da tausayi.

Advertisement

“Shi ba abinda ya sani illa shan giya, duka da kuma takura mini da jima’i kamar ya kashe ni da saduwa kuma ba ruwan sa da ƴaƴan sa. Gaskiya ni na gaji da zama da shi,” in ji ta.

Matar ta kuma roƙi kotu da ta hana Lawal ɗin kiran ta a waya ko kuma zuwa gidan da ta ke.

A nashi ɓangaren, Kawak ya roƙi kotun da ta lallashi Olamide domin ta hakura su ci gaba da zama tare.

Advertisement

“Na tuba, na yi nadama. Na dena shan giya kuma zan ci gaba da kula da ƴaƴa na. Zan canja rayuwa ta,” in ji Lawal, wanda tela ne shi.

Alƙalin kotun, S.M. Akintayo, wanda ya ɗaga zaman sai 3 ga watan Maris domin yanke hukunci, ya shawarci ma’auratan da su zauna lafiya tsakanin su.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *