Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon Janar ɗin sojin Najeriya Birgediya Janar Jonathan Temlong murnar cika shekaru 68 a duniya.
”Tsawon lokacin da ka kwashe kana aiki a matsayin soja, ka nuna tsantsar kishin ƙasarka, don haka ina taya ka da iyalanka murnar zuwan wannan rana” inji Buhari cikin wata sanarwar fadar shugaban ƙasa.
Ya kuma lasafto wasu manyan kyaututtukan girmamawa da tsohon Janar ɗin ya samu lokacin da yake bakin aiki.
Shugaba Buhari ya ce a matsayin Janar Temlong na magoyin bayan gwamnatinsa, yana fatan cewa Janar ɗin zai ci gaba da ba su shawara kan harkar tsaro da daƙile fitintunu.