News
Yadda fashewar nakiya ta hallaka sojojin Nijar huɗu
Dafa kabiru basiru fulatan
A jamhuriyyar Nijar, rahotanni daga Tillabery da ke yankin yammacin kasar – jiha mai iyaka da Mali da kuma kasar Burkina Faso – sun ruwaito da cewa, jami’an tsaro huɗu sun rasa rayukansu, wasu biyu kuma sun tsira da munanan raunuka.
Wannan lamari dai ya wakana ne a jiya Juma’a, bayan motar da jami’an tsaro ke ciki ta taka wata nakiya da aka dasa a kan hanya.
Lamarin ya faru a tsakanin garuruwan Turundi da Makulandi na jihar Tilaberi mai nisan kilomita 100 daga babban birnin kasar Yamai.
Motar jami’an tsaron ta taka nakiyar ne a daidai garin Dogon karfe, kuma sakamakon binciken wucin gadi da jami’an tsaro suka gudanar ya nuna an dasa nakiyar ne.
Wannan sabon salo na dana nakiya da masu tsattsauran ra’ayin kishin Islama ke yi, ya na haddasa asarar rayuka da dama musamman jami’an tsaro a yankin iyakokin kasashe uku wato Burkina Faso da Mali da kuma da jamhuriyar ta Nijar, kuma duk kokarin BBC domin jin ta bakin jami’an tsaro ya ci tura.
Ana samun karuwar kaiwa jami’an tsaron jamhuriyar Nijar hari, ko dai ta hanyar dasa nakiya ko kuma yi musu kwantan bauna da bude um su wuta.